Shugaban Faransa zai kai ziyara Burtaniya – DW – 07/06/2025
Wannan ziyara na da nufin karfafa dangantakar Burtaniya da sauran kasashen Turai bayan ficewar kasar daga Tarayyar Turai a ranar daya ga watan Fabrairun 2020.
Sarki Charles III ne ya gayyaci Shugaba Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte zuwa wannan ziyarar ta kwanaki uku, wato daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan wata na Yuli.
A ranar Alhamis, Macron zai gudanar da tattaunawa tare da Firaministan Burtaniya Keir Starmer a taron kolin Faransa da Burtaniya karo na 37, inda za a mayar da hankali kan tallafin Ukraine da yaki da shige da fice na ba bisa ka’ida ba, da ma batun karfafa tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Ziyarar Shugaba Macron ce ta farko ta wani shugaban kasa na Tarayyar Turai zuwa Burtaniya tun bayan ficewar Burtaniyar daga EU.
Share this content:
Publicar comentário