Shugaban Faransa zai kai ziyara Burtaniya – DW – 07/06/2025

Shugaban Faransa zai kai ziyara Burtaniya – DW – 07/06/2025

Wannan ziyara na da nufin karfafa dangantakar Burtaniya da sauran kasashen Turai bayan ficewar kasar daga Tarayyar Turai a ranar daya ga watan Fabrairun 2020.

Sarki Charles III ne ya gayyaci Shugaba Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte zuwa wannan ziyarar ta kwanaki uku, wato daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan wata na Yuli.

A ranar Alhamis, Macron zai gudanar da tattaunawa tare da Firaministan Burtaniya Keir Starmer a taron kolin Faransa da Burtaniya karo na 37, inda za a mayar da hankali kan tallafin Ukraine da yaki da shige da fice na ba bisa ka’ida ba, da ma batun karfafa tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Ziyarar Shugaba Macron ce ta farko ta wani shugaban kasa na Tarayyar Turai zuwa Burtaniya tun bayan ficewar Burtaniyar daga EU.

Share this content:

Mais de 40 anos de excelência em análises técnicas de petróleo, combustíveis e fluidos industriais. Com mais de 2.000 ensaios, atendemos refinarias, termelétricas, aviação e offshore com precisão, agilidade e interpretação técnica dos resultados. Garanta qualidade, evite paradas e reduza riscos operacionais. Fale com nosso especialista: 📲 (19) 97157-2241 📧 comercial@texasoiltech.com.br